OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zulum a jihar Bauchi, ya jajanta wa Gwamna Bala bisa rashin dan uwan sa

Zulum a jihar Bauchi, ya jajanta wa Gwamna Bala bisa rashin

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar ta'aziyya ga gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed bisa rasuwar dan uwan sa.

Marigayin, Bappa Mohammed ya rasu ne a makon da ta gabata bayan ya sha fama da jinya, kuma tun daga nan aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Marigayin ya rasu ne a lokacin da Gwamna Zulum yake kasar waje.

Kafin rasuwar sa, Mohammed ya kasance mataimakin darakta mai ritaya a babban bankin Najeriya (CBN).

Gwamna Zulum ya samu tarba a gidan gwamnatin jihar Bauchi daga gwamnan jihar Mohammed.

Zulum ya bayyana cewa yana da kyau ya zo da kan sa domin mika ta’aziyyar sa ga gwamna Mohammed, yana mai jaddada cewa marigayin kuma dan uwan sa ne.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau ya fitar a daren Lahadi, gwamnan ya roki Allah ya sanya marigayi Bappa a cikin Aljannar Firdausi.

A cewar sanarwar: “Gwamna Mohammed ya gode wa Zulum bisa wannan ziyara da ya kai masa, ya kuma ce yaji dadin nuna ‘yan uwantaka matuka da Zulum ya masa.

"Ya bayyana Zulum a matsayin wanda ke da kyakkyawan halayen shugabanci na musamman."

Zulum da tawagar sa sun bar jihar da yamma.

Tawagar Gwamna Zulum sun hada da: Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkareem Lawan, Dan Majalisar Dokokin Jihar Borno mai wakiltar Kukawa, Alhaji Haruna Kukawa, Dan Takarar Jam’iyyar APC na Marte, Monguno, Mazabar Tarayya Nganzai a Majalisar Wakilai, Engr Bukar Talba da sauran jigajigan gwamnatin sa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci