OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Uwargidan shugaban kasa ta jajantawa Fubara da iyalan wadanda suka rasu a fashewar tankar mai

Uwargidan shugaban kasa ta jajantawa Fubara da iyalan wadand

Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta jajantawa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar mai a Fatakwal a ranar Juma’a.

 

 A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Bukola Kukoyi, uwargidan shugaban kasar ta bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki da ban tausayi. 

 

“Ina mika ta’aziyyata ga Gwamna Fubara, da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu a mummunan fashewar tankar dakon man fetur da kuma daukacin al’ummar da wannan bala’i ya shafa. Rasa rayuka a cikin irin wannan hanya kwatsam abin ban tausayi ne. Tunanina da addu'o'i na suna tare da su baki" 

 

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce mutane hudu da motoci sama da 70 sun kone a fashewar tankar a ranar Juma'a. 

 

Fashewar, kamar yadda rundunar ta bayyana, ta afku ne a yankin Eleme na hanyar Gabas zuwa Yamma a jihar da misalin karfe 7:30 na yamma, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Grace Iringe-Koko, ta ce lamarin ya faru ne biyo bayan wata arangama da aka yi tsakanin wata babbar mota mai nauyi da tankar man fetur. 

 

Fubara, wanda ya ziyarci wurin da hatsarin ya faru, ya bayyana lamarin a matsayin "abin takaici da bakin ciki." Ya bukaci masu ababen hawa da su rika yin hattara yayin da suke kan hanya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci