OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Guguwa ta lalata makarantar firamare a Nasarawa

Guguwa ta lalata makarantar firamare a Nasarawa

Wata guguwa mai karfi da ta yi barna a makarantar firamare ta LGEA, Gudige Sabo da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Nasarawa tayi sanadiyar dakatar da karatun daliban inda suka dawo karatu a karkashin bishiyu.

 

Guguwar wadda ta auku a ranakun Alhamis da Lahadi, ta lalata ajujuwa, dakin jarrabawa da sauran kayan aiki a firamaren hadi da makarantar Sakandaren GSS, Gudige Sabo dake gudanar da karatu a matsayin wucin gadi.

 

 Kansila mai wakiltar mazabar Ara II a majalisar dokokin Nasarawa, Richard Gupada, a ranar Litinin ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kawo musu dauki. 

 

Ya jajanta wa ma’aikatan da daliban makarantar kuma ya bukace su da su yi hakuri yayin da yake “aiki don nemo maganin halin da ake ciki”.

 

 Kansilan ya koka da yadda a halin yanzu makarantar bata da dakin jarrabawa domin amfanin daliban da suka kammala karatu za su fara jarrabawar kammala Sakandare.

 

"Ya kamata gwamnati da sauran hukumomin da abin ya shafa su kawo mana agaji domin yaranmu ba su da ajujuwa da dakin jarrabawa. Mun riga mun shiga damina, tarbiyyar ‘ya’yanmu a halin yanzu tana cikin hadari ba tare da ajujuwa ba,” ya kara da cewa., SSCE. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci