OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

CBN zai sayarwa yan chanji Dala 10,000 akan Naira 1,021

CBN zai sayarwa yan chanji Dala 10,000 akan Naira 1,021

Babban Bankin Najeriya ya amince da siyar da karin dala 10,000 zuwa ga yan kasuwar chanji BDCs 1,583 a fadin kasar don magance karancin ta a kasuwa.

Dr. Hassan Mahmud, Daraktan Sashen Ciniki da canjin kudi na Babban Bankin Najeriya CBN ne ya bayyana hakan cikin wata wasika da ya aikewa shugaban kungiyar yan canji ta kasa (ABCON) ranar Talata a Abuja. 

A cewar Mahmud, CBN zai sayar da kowace dalar ga BDCs akan kudi N1,021. 

Ya ƙayyade cewa ana sa ran Yan kasuwar bayan fagen bazasu kara ribar da ya wuce kashi 1.5 bisa dari akan yanda suka saya ba.

Mahmud ya umurci duk masu sana'ar chanjin da suka cancanta su fara biyan kudaden ajiya na Naira zuwa lambobin asusun ajiya na CBN.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasar ya bayar da rahoton cewa, a ranar 8 ga watan Afrilu daya gabata babban bankin ya amince da sayar da dala 10,000 ga ma’aikatan BDC 1,588 da suka cancanta a kan kudi N1,101 kan dala. 

Amincewar wani bangare ne na shiga tsakani da CBN ke yi a kasuwar canji domin inganta harkokin kudi da daidaita darajar Naira.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci