OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojoji Sun Ceto Wasu Ƴan Matan Chibok Biyu a Borno

Sojoji Sun Ceto Wasu Ƴan Matan Chibok Biyu a Borno

Photo Source: Daily Post

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa an kuɓutar da wasu ƙarin ƴan matan Chibok biyu, Yana Pogu da Rejoice Sanki a Borno.

Kwamandan rundunar Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar.

Babban jami’in runduna ta 7 dake Maiduguri, Manjo Janar Shu’aibu Waidi, wanda ya gabatar da su ga manema labarai, ya ce za a miƙa su ga gwamnatin jihar Borno, bayan an duba lafiyarsu.

Waidi ya ce an kuɓutar da Pogu mai lamba 19 a jerin sunayen ƴan matan Chibok da aka sace a ranar 29 ga Satumban 2022 tare da yara huɗu.

Jaridar Punch ta tattaro cewa an kuɓutar da yara huɗun wanda suka haɗa da yara biyu maza da tagwaye, a kauyen Mairari, a karamar hukumar Bama, da dakarun soji na 2 a yayin wani sintiri na share fage.

“Hakazalika, a ranar 2 ga Oktoba, 2022, Rejoice Sanki, wacce ke lamba 70 a jerin ƴan matan Chibok, sojojin bataliya ta 222 a yankin Kawuri sun ceto Rejoice Sanki, tare da ƴaƴanta guda biyu.

Ya kara da cewa matan da aka ceto ana duba lafiyarsu tare da ƴaƴansu domin miƙa su ga gwamnatin jihar Borno.

Musa, wanda ya kuma sanar da bude wani sabon sansanin karɓar tubabbun ƴan Boko Haram da ke miƙa wuya, ya ba da tabbacin cewa sabon sansanin na cikin wani wuri mai tsaro da sojoji za su iya tsare shi.

"Bisa kimantawa, mun kalli wuraren da za a iya kare su yadda ya kamata," in ji Musa.

 A cikin watanni biyar da suka gabata sojoji sun ceto ƴan matan Chibok 13,  Ya zuwa yanzu, daga cikin ƴan mata 276 da aka sace a shekarar 2014, kusan 96 ne ke hannunsu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai