OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Hukumar DSS ta ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a Sokoto

Hukumar DSS ta ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a

Rundunar ‘yan sandan farin kaya (DSS) reshen jihar Sokoto ta yi gaggawar ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su cikin sa’o’i 24 a kauyen Gundungul. 

 

Abdulfatah Olawuno, Daraktan DSS na Sokoto, ya ce jami'an hukumar sun Kai dauki bayan al'ummar kauyen sunyi musu kiran neman daukin gaggawa. Sai dai ‘yan fashin sun gudu cikin daji tare da mutanen kauyen da aka sace. 

 

Jami’an DSS sun bi su tare da samun nasarar kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

 

Tuni ‘yan bindigar sun kashe wasu yan kauyen biyu a kauyen Gundungul kafin su yi awon gaba da sauran mutanen bakwai da aka ceto.

 

An duba lafiyar wadanda aka ceto kafin hukumar DSS ta mika su ga gwamnatin jihar.

 

 Sakataren gwamnatin jihar, Muhammad Bello Sifawa, ya yabawa hukumar ta DSS kan wannan bajinta da ya bayyana a matsayin abin farin ciki.

 

Ya kuma tabbatar wa da hukumomin tsaro a jihar cewa gwamnatin na ci gaba da bayar da goyon baya don tabbatar da cikakken tsaro a jihar

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci