OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Jihohi uku sun rasa wutar lantarki sanadiyar lalata turakan wuta da yan ta'adda sukayi

Jihohi uku sun rasa wutar lantarki sanadiyar lalata turakan

Kamfanin dakon wutar lantarki na Najeriya, (TCN) ya tabbatar da cewa yan ta'adda sun lalata turakan wutar lantarki guda hudu da ke kan hanya Jos-Gombe, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki a Jihohi uku na Adamawa, Gombe da Taraba. 

 

Babban jami'in hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Litinin, ya ce an lalata cibiyar wutar da misalin karfe 3:32 na yammacin ranar Litinin. 

 

Sanadiyar hakan wutar lantarki a tashoshin Gombe, Yola, da Jalingo ta lalace, lamarin da yayi sanadiyar yanke wutar lantarkin da ake samu a sassan Yola da Jos.

 

TCN ya bayyana an lalata layin sadarwa na Jos – Gombe 330kV da misalin karfe 3:32 na rana a ranar 22 ga Afrilu 2024. 

 

“TCN ta lura cewa lokacin da layin wutar lantarki mai karfin 330kV ya yi karo, ma’aikatansa sun yi yunkurin mayar da shi aiki amma abin ya sake rugujewa, lamarin da ya sa aka tura mutanen layin TCN don gano layin da kuma gyara kuskuren. Bincike ya nuna cewa an lalata turakai masu lamba 288, 289, 290, da 291"

 

“A halin yanzu, wutar lantarki mai yawa a tashoshin Gombe, Yola, da Jalingo ta lalace, lamarin da ya yi illa ga yawan wutar lantarkin da ake samu a sassan Yola da Jos masu rarraba wutar lantarki ga kamfanonin rarraba wutar lantarkin na Jos, domin rage tasirin lamarin ga masu amfani da wutar da lamarin ya shafa TCN tana kokarin dawo da wuta Gombe ta hanyar isar da wutar lantarki mai karfin 132kV dake Bauchi daga bisani kuma zamuyi kokarin kai wuta ga Ashaka, Potiskum, Damaturu, da Billiri/Savannah"

 

"Za mu yi duk mai yiwuwa don maido da wadatar wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa yayin da muke kokarin gyaran turakan wutan guda hudu da aka lalata," in ji kakakin TCN.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci