OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Jami’ar Ibadan za ta kaddamar da dalibai 3,749 da sukayi nasarar shiga jami'ar

Jami’ar Ibadan za ta kaddamar da dalibai 3,749 da sukayi n

Dalibai dubu uku da dari bakwai da arba’in da tara wadanda suka yi nasarar cika sharuddan shiga jami’ar Ibadan ne ake sa ran za su halarci bukin kaddamarwar na shekarar 2023/2024 da aka shirya gudanarwa a yau Talata, 23 ga Afrilu, 2024. 

 

Kafar Allnews.ng ya tattaro cewa a wannan karon za'a yi taron ta kafar intanet, mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Kayode Adebowale, zai bude taron tare da gabatar da jawabi yayin da aka umurci mahalarta taron su shiga yanar gizo da karfe 10 na safe don fara bikin.

 

Dr. Victor T. Alabi, na sashen nazarin harshe a Jami'ar Brown, dake Amurka zai gabatar da mukala yayin bikin inda Magatakardan jami'ar, Mista G. O. Saliu, zai kaddamar da sabbabin daliban.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci