OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Majalisar dattawa ta bayyana damuwa akan yawan faduwar darajar Naira

Majalisar dattawa ta bayyana damuwa akan yawan faduwar daraj

Nasarawa State House of Assembly

Sanata Sani Musa mai wakiltar Neja ta Gabas kuma mai rike da mukamin shugaban kwamitin harkokin kudi a majalisar ya nuna damuwarsa game da faduwar darajar Naira idan aka kwatanta da kudaden kasashen waje. 

 

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar mai taken “Halin da tattalin arzikin kasa ya shiga da faduwar darajar Naira,” Sanata Musa ya jaddada bukatar hadin gwiwa daga masu ruwa da tsaki wajen magance matsalar yawan faduwar darajar kudin. 

 

Ya kuma danganta faduwar darajar Naira da wasu abubuwa da suka hada da; sauye-sauyen farashin mai a duniya, gibin kasafin kudi, da rashin daidaiton a tsarin tattalin arziki. 

 

Sanata Musa ya jaddada bukatar yin gaggawar aiwatar da matakan da suka dace don kiyaye dorewar darajar Naira.

 

 Ya kuma kara jaddada aniyar kwamitin kudi na majalisar dattawa na sa ido sosai kan lamarin da kuma yin aiki tare da masu ruwa da tsaki don aiwatar da ingantattun manufofi. 

 

 “Kwamitin kudi na majalisar dattijai yana binciko hanyoyin da za a bi don dakile tasirin faduwar darajar Naira da samar da daidaiton tattalin arziki. Wannan ya hada da sanya ido sosai kan manufofin kasafin kudi, hada hannu da manyan masu ruwa da tsaki, da kuma samar da hanyoyin farfado da tattalin arziki". 

 

Ya kara da cewa "ina kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su zama masu juriya. Tare, za mu iya shawo kan kalubalen da tattalin arzikinmu ke fuskanta tare da tsara hanyar samar da wadata ga kowa da kowa."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci