OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

"Na Tsani Aure" Cewar Matar Da Ta Kashe Mijinta Da Guba a Borno

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta kama wata matar aure mai suna Fatima Abubakar bisa zargin kashe mijinta, Goni Abbah da guba.

Matar wadda batafi shekaru 25 ba, ta kashe mijinnata ne wanda shi ne Babban Limamin yankin bayan ya dawo daga masallaci.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Abdu Umar ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Maiduguri, babban birnin jihar.

Umar ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 19 ga watan Oktoba a Anguwan Doki wadda kuma ta kasance matar marigayin ce ​​ta biyu.

Ya ƙara da cewa bayan matar ta zuba guba a abinci, Abbah ya fara cin abincin kenan sai ya fara jin ba daɗi.

A cewarsa, nan take aka garzaya da marigayin zuwa asibitin kwararru na jihar inda aka ba shi kulawa amma daga baya ya rasu.

Kwamishinan ƴan sandan yace wacce ake zargin ta amince da aikata laifin, inda ta ce ta sayi gubar ne daga kasuwa bayan ta yanke shawarar kashe mijinta.

Ta ce, “Ban taɓa son auren ba, Goni shine mijina na biyu, Na rabu da mijina na farko saboda na tsani aure.

“A duk lokacin da na farka na tuna cewa na yi aure, abin yana ban haushi, cewar Jaridar Punch.

"Wani lokaci sai na ruga wurin iyayena don neman a raba auren, amma kullum sai su mayar da ni, suna cemin na yi haƙuri.

“A wani lokaci, bayan wata biyu da na haifi ɗa na, sai na gudu na kwanta a wani ginin da ba'a kammala ba na kusan sati biyu, Daga baya na koma gidan mijina.

“Ba wai ba ya kyautata min bane, kuma ba rigima muke yi ba, Mu biyu ne a gidan, ni ce matarsa ​​ta biyu kuma na aure shi tun 2021, Amma ni dai na tsani inga kowane namiji ya zo kusa da ni.

“Ban san ainihin abin da ke damuna ba, Ko yanzu da nake magana da ku, ba na jin cewa ni ne na kashe shi.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci