OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Jamb zata saki sakamakon jarabawar 2024

Jamb zata saki sakamakon jarabawar 2024

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta kammala shirye-shiryen fitar da sakamakon jarrabawar ta shekarar 2024. 

 

Magatakardar hukumar Farfesa Ishaq Oloyede,ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin mai zuwa.

 

 Shugaban hulda da jama’a na hukumar Fabian Benjamin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata ta nuna alamar za a fitar da sakamakon jarabawar a ranar Litinin.

 

Za'a fara sakin sakamakon jarabawar daliban da suka fara rubuta jarabawar a kwanakin farko, yayin da wadanda suka rubuta jarabawar a kwanikin karshe za a saki sakamakonsu daga baya. 

 

Tun da farko dai hukumar ta bayyana cewa an yanke shawarar jinkirta fitar da sakamakon na wasu kwanaki ne domin a ba da isasshen lokaci domin tantancewa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci