OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kasar Kanada ta ba da tallafin $3m don tallafa wa kiwon lafiya a jihar Bauchi

Kasar Kanada ta ba da tallafin $3m don tallafa wa kiwon lafi

Gwamnatin kasar Canada ta sanar da bayar da tallafin dala miliyan uku ga gwamnatin jihar Bauchi domin bunkasa harkokin mata a bangaren kiwon lafiya.

 

Shugaban Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, reshen jihar Bauchi, Tushar Rane, ya bayyana hakan ne a lokacin da wata tawagar hadin gwiwa ta UNICEF da Global Affairs Canada suka ziyarci Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ranar Talata a Bauchi.

 

Ya ce an ba da tallafin kudin ne don karfafawa mata ta hanyar ba su damar shiga harkokin kiwon lafiya don cin moriyarsa.

 

UNICEF ta aiwatar da wannan aikin ta hanyar haɗin gwiwar MoU yayinda ita kuma Gwamnatin Kanada ta ƙaddamar da hidimar aikin ga UNICEF.

 

Za mu yi aikine da Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi da sauran abokan hadin gwiwa sannan kuma za mu yi aiki a dukkan sassan 323 na jihar domin ba wa mata damar cin moriyar ayyukan kiwon lafiya,inji shi.

Daily Nigeria Ta Ruwaito

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci