OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Borno: Sojoji Sun Kashe ''Yan Ta'addan ISWAP 31, Sun Kama 70

Borno: Sojoji Sun Kashe ''Yan Ta'addan ISWAP 31, Sun Kama 70

Sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun kashe 'yan ta'addan ISWAP 31 tare da kama wasu 70 a jihar Borno.

Kakakin hedkwatar tsaro Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a yau (Alhamis).

Danmadami ya ce daga cikin mutane 70 da aka kama, 60 ne masu samar wa 'yan ta'addan kayan masarufi da suka hada da hatsi, alburusai, mai da sauran abubuwa.

Ya kara da cewa sojojin sun kuma ceto wasu fararen hula biyu daga hannun ‘yan ta’addan yayin da 'yan ta'addan 366 tare da iyalan su suka mika wuya.

Ya ci gaba da cewa, a ranar 11 ga watan Oktoba ne sojojin suka fatattaki ‘yan ta’addan da suka yi wa sojoji kwanton bauna wanda ya kai ga halaka ‘yan ta’adda 18.

Sojojin sun kuma gano tarin makamai a yayin harin.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, Danmadami ya ce: “A dunkule, a cikin makonnin da aka gudanar da aikin, sojojin sun kwato bindigogi kirar AK47 guda 14, GPMG guda biyu, bindigar M21 daya, bam mai lamba 125mm daya, harsashi 40 na musamman na 7.62mm, wasu bindigogi guda shida, bindiga guda daya na gida, mota daya, wayoyin hannu hudu, kekuna biyar da babura 11.

“An kuma gano buhunan wake 64, buhunan masara guda biyar, wasu abubuwa masu yawa da ake zargin wiwi ne.

“Kayan magani, kayan sawa iri-iri, Dabbobi 46, Naira 250,000 da sauran kayayyaki iri-iri.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci