OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yobe Ta Arewa: Ba Zan Ɗaukaka Ƙara Ba, Cewar Ahmad Lawan

Yobe Ta Arewa: Ba Zan Ɗaukaka Ƙara Ba, Cewar Ahmad Lawan

Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce ba zai ɗaukaka ƙara ba akan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Damaturu a jihar Yobe ta yanke.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba ba, dangane da tikitin sanata a mazaɓar Yobe ta Arewa.

Mista Lawan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Alhamis, inda ya ce ya amince da hukuncin da kotun ta yanke wanda ya haramta masa tsayawa takara da kuma shiga zaɓen.

“A jiya Laraba, 28 ga Satumba, 2022, babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta yanke hukunci kan wanda ya cancanta ya tsaya takarar Sanatan Yobe ta Arewa a zaɓen ƴan majalisar tarayya na 2023.

"Hukuncin da aka ce ya hana ni takara da kuma haramtamin shiga zaɓen.

“Bayan tuntuɓar juna da abokaina na siyasa, magoya bayana da kuma masu fatan alheri, na yanke shawarar ba zan ɗaukaka ƙara ba akan hukuncin ba, kuma na yarda da hukuncin.”

Jaridar Punch ta ruwaito Lawan yana yabawa gwamnansa da dan mazaɓar sa bisa goyon bayan da suka ba shi. 

“Ina ganin ya dace in godewa mai girma Sanata Ibrahim Gaidam bisa rawar da yake takawa a siyasar jam’iyyar APC a jihar Yobe.  

"Ina kuma gode wa mai girma Gwamna Mai Mala Buni bisa goyon baya da ƴan uwantaka.

“Ga al’ummar mazaɓana, ina gode muku baki ɗaya bisa goyon bayan da kuka bayar, da biyayya da sadaukarwar da kuka yi na gina al’ummarmu da kuma gundumar Yobe ta Arewa da kuma jihar Yobe.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci