OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kotun ta dage shari'ar Godwin Emefiele

Kotun ta dage shari'ar Godwin Emefiele

Wata babbar kotu da ke zamanta a unguwar Maitama a birnin tarayya Abuja, ta dage shari’ar Godwin Emefiele zuwa ranar 24 ga watan Yuni.

 

 A ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, ya kamata a cigaba da shari'a amman lauyan mai gabatar da kara da wanda ake tuhuma ba su halarci zaman kotun ba sanadiyar daya sa aka daga shari'ar.

 

Barista I.D Ahmed, daya daga cikin lauyoyin Emefiele, ya shaida wa kotun cewa masu gabatar da kara sun mika masa wasikar neman a dage shari’a. Ya kuma nemi afuwar kotu kan rashin halartar wanda yake karewa. 

 

Alkalin kotun, Hamza Muazu ya ce: “Saboda kana da takardar dage shari’ar daga masu gabatar da kara ba yana nufin kada wanda ake kara ya bayyana a gaban kotu.” Daga nan Muazu ya dage shari’ar har zuwa ranar 24 da 25 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraron karar. 

 

Idan za'a iya tunawa a ranar 28 ga watan Janairu, gwamnatin tarayya ta kara adadin laifukan da ake tuhumar Emefiele da aikatawa daga tuhume-tuhume shida zuwa ashirin. 

 

Zarge-zargen da aka yi wa kwaskwarima sun hada da zarge-zargen aikata laifuka, hada baki, zamba, da kuma hada baki wajen aikata laifi.

 

A zaman da ya gabata, kotun ta yanke shawarar sauya sharadin belin Emefiele, wanda a baya ta tsare shi a babban birnin tarayya Abuja, inda kotun ta amince tsohon gwamnan CBN zai iya yin tafiya cikin Najeriya, amma ta hana shi fita daga kasar yayin da ake ci gaba da shari’ar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci