OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Gwamnatin Jigawa ta nada Amirul Hajjin bana

Gwamnatin Jigawa ta nada Amirul Hajjin bana

Jigawa Governor, Umar Namadi

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya amince da kafa kwamitin aikin hajji ta 2024 don tabbatar da gudanar da aikin hajjin bana ba tare da tangarda ba ga maniyyatan jihar. 

 

Gwamnan ya kuma bayyana nadin Mai Martaba Sarkin Hadejia Alhaji (Dr) Adamu Abubukar Maje a matsayin Amirul Hajji na Jiha.

 

 Kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, SSG, Malam Bala Ibrahim ta rawaito a ranar Asabar, Amirul Hajjin zai kuma kasance jagoran tawagar gwamnati wajen gudanar da aikin Hajjin bana.

 

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Alhaji Turaki Ibrahim. Alhaji Nasidi Ali, Alhaji Habibu Ubah Ringim da Dokta Abubukar Sani Birnin Kudu.

 

Sanarwar ta kara da cewa an nada wadannan mutane sanadiyar yarda da akayi da ingancin su, jajircewa, kishin kasa, rikon amana da tsoron Allah (S.W.T)

 

Daga nan sai ya yi kira gare su da su “nuna wadannan halaye wajen gudanar da wannan gagarumin aiki domin sauke nauyin da gwamnatin ta dora musu" 

 

Ana sa ran tawagar Amirul Hajj za ta yi aiki tare da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa da sauran hukumomin da abin ya shafa a matakin Jiha da Tarayya da kuma na kasa da kasa domin gudanar da ayyukan Hajji mai inganci.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci