OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kotu ta aike da dan kasuwar daya sai kayan sata gidan yari na tsawon shekaru biyar

Kotu ta aike da dan kasuwar daya sai kayan sata gidan yari n

Wata kotun majistare dake Ikeja ta yankewa wani dan kasuwa mai suna Mohammed Abdulhamid dan shekara 22 hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari a ranar Litinin bisa samunsa da laifin karban wasu kayayyakin sata da suka kai Naira miliyan 2.19. 

 

Wanda ake tuhumar mazaunin unguwar Ayobo da ke Legas, ya amsa dukkan laifuka biyun da aka tuhumeshi da su da suka hada da hada baki wajen aikata laifi da sayan kayan sata. 

 

Maisharia Misis O. O. Fagbohun ta yanke wa wanda ya aikata laifin hukuncin zuwa gidan yari na Kirikiri, ba tare da zabin biyan tara ba a cewar Fagbohun, hukuncin zai zama izina ga wasu masu muradin aikata makamancin hakan.

 

 Mai gabatar da kara, Insp. Felicia Okwori ta sanar da kotun tun da farko an aikata laifin a watan June 2023 a adereshin 56 Captain Davies Road, Ayobo, Legas.

 

A cewar Okwori, wanda ake kara ya samu kayan sata ne daga hannun Mohammed Awalu, mai gadin mai kara, Omolola Idowu. Ta ce a halin yanzu Awalu na tsare a gidan yari bisa wannan tuhuma. 

 

Ta ci gaba da cewa, a lokacin da mai shigar da karar tayi tafiya, Mai gadin nata ya hada Baki da wasu bata gari ya sace Mata kayan da suka hada da kofifin gate guda biyu da darajar su yakai 540,000, N870,000 na taga, sai kuma N300,000 na kudin injin da dai sauran kayayyaki.

 

Ta bayyana cewa jumular kayayyakin da aka sace sun kai Naira miliyan 2.19. Mai gabatar da kara ta ce laifukan sun sabawa dokar laifuka ta 2015 na jihar Legas sashi na 328 da 411. 

 

A halin da ake ciki kuma, a garin Kafanchan da ke Kaduna, kotun majistare ta bayar da umarnin tsare John Simon da Yusuf Nikie a gidan yari bayan sun amince da satar babur, Alkalin kotun Michael Bawa ya dage yanke hukunci har zuwa ranar 2 ga watan Mayu. 

 

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta gurfanar da Simon da Nikie a gaban kuliya bisa zargin hada baki da sata.

 

 A cewar mai gabatar da kara Marcus Audu, Tanko Umaru ya shigar da kara a ofishin hukumar da ke Kafanchan a ranar 13 ga Afrilu. Audu ya ce wadanda ake tuhumar sun shiga gidan mai karar da ke Bakin Kogi suka sace babur din sa na Bajaj. Ya ce an kama wadanda ake tuhumar ne a yayin gudanar da bincike, kuma an gano babur din a hannunsu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci