OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Akinterinwa ya zargi Ododo dayin magudi a zaben fidda gwannin da aka kammala a Ondo

Akinterinwa ya zargi Ododo dayin magudi a zaben fidda gwanni

Daya daga cikin yan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Ondo, Wale Akinterinwa, ya zargi shugaban kwamitin gudanar da zaben fidda gwannin Usman Ododo da yin magudi a sakamakon zaben.

 

 Akinterinwa ya yi ikirarin cewa anyi magudi Kuma sakamakon zaben fidda gwanin da aka kammala a jihar da aka fitar jabu ne.

 

 Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo, ya ayyana gwamna Lucky Aiydatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben.

 

Sai dai a wata sanarwa da kakakin yakin neman zaben Akinterinwa, Segun Ajiboye, ya fitar a safiyar ranar Litinin a Akure, ya zargi gwamnan Ododo da zama ya shirya ya kuma rubuta sakamakon zaben. 

 

Mai neman kujerar gwamnan ya kuma bayyana cewa ayyana Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani tamkar almarace da batai kama da hakikanin abunda ya faru ba wajen kada kuri'a.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci