OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Za'a gudanar da babban taron kungiyar marubuta wasanni a Kano

Za'a gudanar da babban taron kungiyar marubuta wasanni a Kan

A ranar Alhamis 2 ga watan Mayu ne za a gudanar da babban taron kungiyar marubuta wasanni ta kasa SWAN a Kano.

 

Shugaban kwamitin wayar da kan jama’a na taron, AbdulGaffar Oladimeji ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Lahadi. 

 

A cewar sa, taron zai gudana ne a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano.Ya kara da cewa ana sa ran ministan wasanni John Enoh zai bude taron.

 

 Oladimeji ya kara da cewa, "delegate 130 ne zasu halarta da yan majalisar zartarwa kungiyar 17 hadi da tsoffin shugabannin kasa, tsofaffin shugabannin jihohi da sakatarorin gwamnati, da kuma tsoffin yayan kungiyar," 

 

Ya kara da cewa za'a karrama wadanda suka tallafawa bukasar harkokin wasanni a kasar nan kamar tsohon shugaban NFA Ibrahim Galadima, za a karrama shi da lambar yabo ta kungiyar a wajen taron. 

 

Sauran wadanda za'a karrama sun hada da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Baba Halilu Dantiye, da kuma Isyaku Umar Tofa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci