OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Najeriya zata farfado da kadada miliyan hudu domin bunkasa noma

Najeriya zata farfado da kadada miliyan hudu domin bunkasa n

Hukumar Abinci da Noma ta kasa FAO tare da hadin gwiwar shirin farfado da ayyukan gona na ACRESAL sun bayyana aniyar Najeriya na farfado da kadada miliyan hudu na gurbatattun filayen noma.

 

 Shirin ACReSAL yayi alkawarin tallafawa wajen farfado da kadada miliyan daya, yayin da FAO ta sha alwashin amfani da kimiya da fasaha wajen maido da fili mai fadin hekta 350,000.

 

Dokta Dahir Muhammad Hashim, Ko’odinetan ayyukan ACReSAL a Kano ne ya bayyana haka a karshen taron kwana biyar na horar da direbobin injinan garma na Delfino akan gyaran filayen noma da aka gudanar a unguwar Kyale da ke karamar hukumar Gabasawa. 

 

Dokta Hashim ya bayyana cewa tuni aka fara aikin dawo da gurbatattun gonaki sama da hekta 10,000 a fadin jihar, inda ya kara da cewa, “A karkashin shirin ACRESAL, gwamnatin Kano ta gano sama da hekta 10,000 na gurbatacciyar kasa da zata gyra a danka su a hannun manoma domin suyi shuka"

 

 Hakazalika, shirin zai baiwa manoma iri, taki, da sauran kayan amfanin gona don tallafawa samar da abinci.

 

Dakta Hashim ya jaddada muhimmancin dashen itatuwa a filayen da aka farfado dasu domin magance sare bishiyu da kuma bada gudumawa ga kokarin rage dumamar yanayi a kananan hukumomin a jihar Kano.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci