OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Sama da mutum dubu biyu sun kamu da sankarau a Yobe

Sama da mutum dubu biyu sun kamu da sankarau a Yobe

Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa ta sake gano wasu mutane 2,510 da suka kamu da cutar sankarau mai suna Cerebrospinal Meningitis, Type C, daga ranar 25 ga watan Disamba, 2023 zuwa Afrilu, 2024.

 

Gwamnatin Kano ta kara da cewa mutum 85 da suka kamu da cutar sun mutu sakamakon kamuwa da cutar kafin akaisu asibiti.

 

Kwamishinan lafiya Dr Muhammad Lawan Gana ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan bullar cutar a jihar.

 

Yace “Daga watan Disamba zuwa makon da ya gabata, akwai jimillar mutane 2,510 da suka kamu da cutar, inda 85 suka mutu bincike ya nuna cewa ko dai sunje cibiyoyin kula da lafiya ko kuma ba su je ba baki daya. 

 

Ya kara da cewa a cikin makonni biyun da suka gabata, jihar ta sami sabbin mutane 28 da suka kamu da cutar da kuma mutuwar mutane biyu. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci