OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kotu ta jinginar da umarnin dakatar da Ganduje

Kotu ta jinginar da umarnin dakatar da Ganduje

Wata babbar kotu a Kano ta fitar da wani umarnin wucin gadi na jinginar da dakatarwar da aka yi wa Dr Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa.

 

Alkalin kotun mai shari’a Usman Mallam Na’Abba, ya umarci shugabannin Mazaɓar Ganduje da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, kada su yi aiki da umarnin babbar kotun jihar na dakatar da shugaban jam’iyyar.

 

Umarnin Babbar Kotun Tarayyar na zuwa ne awa 24 da babbar kotun jihar ta amince da bukatar shugabannin mazabar ta dakatar da tsohon gwamnan jihar, saboda gwamnatin jihar mai ci na zarginsa da almundahana.

 

Alƙalin ya hana duk waɗanda umarnin kotun jihar ya shafa bin umarnin, har sai ya saurari ƙarar da Ganduje ya shigar gabansa ne neman adalci a saurari ɓangarensa.

 

Kotun ta kuma sanya ranar 30 watan nan na Afrilu domin sauraren buƙatar ta shugaban jam’iyyar kuma tsohon gwamnan Kano.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci