OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

"EFCC haramtacciyar hukuma ce"-Yahya Bello

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, haramtacciyar hukuma ce.

 

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan yayin da ya tsaya gaban babbar kotun tarayya dake Abuja domin amsa tuhume-tuhume 19 da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta shigar a kansa.

 

 Duk da Yahya Bello bai halarci zaman kotun ba na ranar Talata, tawagar lauyoyinsa sun wakilce shi a gaban kotun. 

 

Adeola Adedipe, SAN daya daga cikin lauyoyin sa, ya shaida wa kotun cewa Yahya Bello ya ce yana a tsoron kama shi idan ya bayyana a gaban kotu da kan sa, kamar yadda Allnews.ng ta ruwaito.

 

Ya ci gaba da cewa hukumar EFCC haramtacciyar hukuma ce. A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ba ta tuntubi Jihohi 36 na tarayya ba kafin ta kafa dokar ta EFCC ta hannun Majalisar Dokoki ta Kasa.

 

 Ya ce sashe na 12 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya bukaci Majalisun Dokokin Jihohi daban-daban su amince da dokar kafa hukumar kafin ta fara aiki.

 

Lauyan Yahya Bello ya kara da cewa “Wannan lamari ne mai matukar muhimmanci da ya shafi sahihancin tanadin da kundin tsarin mulki sukayi. Dole ne a warware shi domin a halin yanzu, EFCC haramtacciyar hukuma ce,” 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci