OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan sanda sun kama Yan kungiyar asiri 46 a jihar Kwara

Yan sanda sun kama Yan kungiyar asiri 46 a jihar Kwara

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta cafke mutane 46 da ake zargi da hannu a rikicin kungiyar asiri a jihar. 

 

A cewar rundunar a ranar Litinin, ’yan kungiyar asirin sun yi artabu a karshen mako wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda. 

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan Toun Ejire-Adeyemi ya ce, “Wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun kai hari inda suka kashe Adelodun Farouq mai shekaru 36, mazaunin unguwar Eleran. An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada ba tare da sanin ‘yan sanda ba.

“Bincike ya nuna cewa wani Abubakar Gobir dan kungiyar Ayee confraternity yana da hannu a wannan aika-aika. Daga baya a yammacin wannan rana, rahotanni sun sake bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da fadan yan kungiyar asiri a harabar Ile-Alawo, dake unguwar Centre Igboro." In ji shi.

 

 A ranar 14 ga watan Afrilu, Yan kungiyar asirin sun kai hari a unguwanni Baboko, Ile Onimago, Adabata, da kuma Eruda. 

 

Kakakin rundunar Toun Ejire-Adeyemi ya kuma bayyana "Bata-garin sun yi artabu da muggan makamai kamar fasassun kwalabe da duwatsu, lamarin da ya kai ga toshe hanyar Baboko. DPO na Dibision C ne ya dauki matakin gaggawa, da hadin gwiwwar tawagar ‘yan sintiri guda shida,sun dauki matakin shawo kan lamarin. A yayin aikin, an kama mutane 46, kuma an mika su ga sashin yaki da ‘yan kungiyar asiri na rundunar domin ci gaba da bincike."

 

 Daga cikin mutane 46 da aka kama, 14 na da alaka da ayyukan kungiyar asiri da aka samu a yan kwanakin nan a cikin babban birnin Ilorin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci