OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Rundunar Yansanda ta kama ADC din Yahaya Bello

Rundunar Yansanda ta kama ADC din Yahaya Bello

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama jami'an da ke kula da tsaron tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

 

An kama ADC din tare da wasu jami’an ‘yan sanda da ke da alaka da tsohon gwamnan kamar yadda jaridar Dailypost ta ruwaito.

 

An kama jami’an ne bisa zarginsu da taimakawa Bello wajen tserewa daga hannun jami’an hukumar EFCC din da sukayi kokarin kamashi a gidansa dake Abuja a ranar Laraba.

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta sanar da neman Yahya Bello ruwa a jallo, inda ta bukaci ‘yan Najeriya masu cikakken bayani game da inda ya ke da su kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.

 

Sfeto Janar na ‘yan sanda, Olukayode Egbetokun a ranar Alhamis da daddare ya ba da umarnin a janye duk jami’an da ke yiwa Yahya Bello aiki.

 

 Umurnin janye Yan sandan ya biyo bayan bacewar Bello daga gidansa da ke Abuja bayan hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta yiwa gidan kawanya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci