OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan sanda sun kama mutum hudu da suka kashe wata mata domin yin tsafi a Osun

Yan sanda sun kama mutum hudu da suka kashe wata mata domin

An kama wasu mutane hudu da ake zargi da laifin kashe wata mata mai shekaru 45 a Ibadan, jihar Oyo. 

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ce ta kama su tare da yin holen su a ranar Juma’a a Osogbo babban birnin Jihar.

 

 Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Yemisi Opalola ce ta bayyana hakan a yayin holen wadanda ake zargin a Osogbo.

 

SP yemisi tace sun kama su ne bayan sun samu rahoton batan matar daga bakin dan ta.

 

“A ranar 18 ga Maris, dan marigayiyar ya kawo rahoto ofishin yan sanda dake Apomu cewa a ranar 13 ga Maris, da misalin karfe 10 na safe, mahaifiyarsa, Aminat Usman, mai shekaru 45, ta bar gida zuwa Lyana Ajia-Ibadan, jihar Oyo, domin kai ziyara ga wani mai bada maganin gargajiya Onifade Oyekanmi". 

 

Ya bayyana cewa tun lokacin da mahaifiyarsa ta bar gida, wayoyinta a kashe suke, ba a san inda take ba, kuma ya yi zargin cewa Mai magani Oyekanmi, yana da masaniya akan bacewar mahaifiyarsa. 

 

Daga baya an kama Onifade Oyekanmi, sannan aka mika shi zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar Osun, domin tsarara bincike" inji ta. 

 

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, Mai maganin ya amsa lefin sa kuma ikirari da wanda ake zargin ya yi ne ya kai ga kama wasu mutane uku, wadanda dukkansu sun bayyana irin rawar da suka taka a wajen kashe matar don yin tsafi da sassanta ta su samu dukiya.

 

 “yayin binciken harabar gidan wadanda ake zargin, an samu kwalabe uku dauke da bakaken abubuwa da ake zargin konanan sassan jikin mutane ne, da wata babbar bakar tukunyar tabo hadi da wasu bakaken sabulai,” in ji kakakin ‘yan sandan.

 

 SP Yemisi ta ci gaba da cewa, an kama wata mace makwabciyar daya daga cikin wadanda ake zargin, wadda ta taimaka masa wajen boye kasonsa na wani garin hoda da zaiyi tsafin da ita, amma daga baya aka bayar da belinta saboda tana shayar da jariri dan watanni hudu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci