OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

An kama fursunoni 14 daga cikin 119 da suka tsere daga gidan yarin Suleja

An kama fursunoni 14 daga cikin 119 da suka tsere daga gidan

An sake kama mutum 14 daga cikin fursunoni sama da 100 da suka tsere daga gidan ajiya da gyaran halin Suleja a jihar Neja sakamakon rusau din da mamakon ruwan sama yayi.

 

Adamu Duza, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen babban birnin tarayya, ya tabbatar da sake kama mutanen, yana mai cewa ana ci gaba da kokarin cafke sauran wadanda suka tsere.

 

 “Ya zuwa yanzu an sake kama fursunoni 14 da suka tsere. Har yanzu dai ana ci gaba da bincike,” kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito Mista Duza yana fadar haka a ranar Alhamis din da ta gabata.

 

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa bangarori daban-daban na jami’an tsaro na aiki tare, wajen binciken unguwannin dake kusa da gidan yarin domin ganin an sake kame fursunonin da suka gudu.

 

“Jami’an leken asirin mu, jami’an rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar DSS, da sauran jami’an tsaro, suna cigaba da bincike domin gano fursunonin da suke gudu,” inji shi. 

 

Mammakon ruwan sama mai karfi ne ya rusa katangar da ke kewayen gidan yarin, wanda ya baiwa fursunoni 119 damar tserewa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci