OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwanatin Kwara ta rufe mayanka bisa zargin sayar da nama mai guba

Gwanatin Kwara ta rufe mayanka bisa zargin sayar da nama mai

Gwamnatin jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe mayankar da ke kasuwar Mandate a Ilorin, karamar hukumar Ilorin ta yamma har zuwa ranar Laraba.

 

Hakan ya biyo bayan zargin sayar da naman saniya mai guba a kasuwar.

 

 Ma’aikatar Muhalli a cikin wata sanarwa da ta babban sakataren ta Dr. Abubakar Ayinla ya fitar a ranar Lahadi ta kuma ba da umarnin tsaftacewa da yiwa mayankar feshin magani domin wanke dukkan sinadarin da ka iya zama guba a jikin dan Adam. 

 

Ayinla ya ce matakin ya biyo bayan korafin wata kungiya mai zaman kanta mai suna Kwara Monitoring Group cewa naman shanu 33 da ake zargin sun mutu sakamakon guba ya samu shiga mayankar domin siyar da su. 

 

‘Yan kungiyar, a wata sanarwa a safiyar ranar Lahadi, ta yi zargin cewa: “Sama da shanu 33 da ake zargin sun ci guba sun mutu nan take amma an yanka matattun dabbobin aka raba ga mahauta domin a sayar da su. Lamarin ya faru ne a kan titin Atere cikin Kwalejin Larabci da Ilimin Addinin Musulunci, Ilorin. Muna fatan ma’aikatar da hukumar da abin ya shafa su dauki matakin gaggawa domin babu wanda ya san adadin wadan da zasu sayi irin wannan nama mai guba"

 

A martanin da gwamnatin jihar ta fitar, a wata sanarwa da ta sanya wa hannu kwamishiniyar lafiya Dr Amina El-Imam da takwaranta na ma’aikatar noma, Toyosi Adebayo, sun ce sun tura tawagar jami’ai zuwa mayankar inda suka ce sun kama naman da ake zargin yana da guba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci