OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Ofishin 'Yansanda a Imo, Sun Kashe Mutum Daya

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Ofishin 'Yansanda a Imo, Sun

Hoto Daga: PremiumTimes

A wani hari da 'yan bindiga suka Kai ofishin 'yansanda dake Arondizuogu da ke karamar hukumar Ideato ta Arewa a jihar Imo, sun kashe wani dansanda tare da raunata wasu.

Har yanzu dai ba'a san 'yan bindigan ko su waye ne ba.

A halin yanzu babban jami'in 'yansandan ofishin (DPO) yana asibiti don yin jinya.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun kai harin ba-zata ne da misalin karfe biyu na safiyar Talata.

Yayin da suka kai harin, sun kashe dansanda daya tare da kona motoci har da na DPO.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Imo, Michael Abattam ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Abattam ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Rabiu Hussaini, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan harin.

 

Jihar Imo na cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro a kudancin Najeriya inda ake kai hare-hare kan jami'an gomnati.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci