OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan bindiga sun kashe wani basarake a Taraba

Yan bindiga sun kashe wani basarake a Taraba

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe basaraken masarautar Sansani da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, Alhaji Abdulmutalib Jankada. 

 

Maharan dauke da makamai ne sun kutsa cikin gidan basaraken a daren ranar Alhamis suka harbe shi har lahira.

Jaridar Daily trust ta rawaito wata majiya na cewa maharan sun isa garin Sansani ne a kan babura Inda suka kutsa cikin fadar sarkin cikin dabara suka kuma yi lugudan wuta a turakar basaraken, bayan sun tabbatar da ya mutu sun sace masa wayoyinsa baki daya kafin iyalansa da jami'an tsaron fadar su farga.

 

Musa Sansani, wani mazaunin garin Sansani, ya ce sun ji karar harbe-harbe amma ba su san cewa daga fadar suka fito ba. 

 

“Marigayi sarki ya shaida mana a jiya cewa zaiyi tafiya zuwa Ibbi domin bikin kamun kifi na Nwonyo, wanda ke gudana a ranakun Juma’a da Asabar. Saboda haka bamuyi tsammanin Yana cikin fadar ba a lokacin da muka jiyo karar harbi" Musa ya shaida wa manema labarai. 

 

Rahotanni sun bayyana cewa matarsa ce ta gano gawar sa a dakinsa, ta sanarwa da sauran mutanen garin da ma sarakunan makwabtan garuruwa.

 

 "Muna matukar jimamin mutuwar mai martaba sarki kuma za a binne shi bayan sallar Juma'a," in ji Musa Sansani

 

Idan za'a iya tunawa dai an taba yin garkuwa da marigayin a hanyar Jalingo zuwa Wukari shekaru biyu da suka gabata, kuma saida aka biya kudin fansa kafin a sako shi.

 

Sarkin Sansani shine basarake na bakwai da yan bindiga suka kashe a yan shekarun nan a yankin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci