OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Takarar Tinubu Ya Saɓawa Doka, Cewar PDP

Takarar Tinubu Ya Saɓawa Doka, Cewar PDP

Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta ce halaccin ɗaukar nauyin  takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya saɓawa doka kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanada.

Sakataren yaɗa labarai na jam'iyar Debo Ologunagba ne bayyana haka yayin hirarsa da manema labarai a ranar Asabar.

Ologunagba ya jaddada cewa hukuncin kotu na baya-bayan nan da ya soke dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala kwanan nan, Adgeboyega Oyetola na iya haramta takarar Asiwaju Bola Tinubu.

A wata zantawa da manema labarai a Abuja, wanda wakilin Punch ya tattaro a shafinsa na Facebook, Ologunagba ya yi ikirarin cewa APC ta aikata haramtattun abubuwa da ya kamata a soke ƴan takarkarinsu.

Yace haramtacciyar rawar da kwamitin riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, wanda kuma ya kasance gwamnan jihar Yobe, ya sabawa doka bisa sashe na 183 na dokar zaɓe.

“Mai Mala Bala ana zaton shi ne Shugaban jam’iyyar APC, kuma doka ta ce idan kai gwamna ne mai zartaswa ba za ka iya zama shugaba ba. 

"Hakan ya sa kotu ta soke takarar gwamnan jihar Osun, Oyetola.

“Mai Mala Buni shi ne shugaban riko wanda ya dauƙi nauyin tantance Tinubu.  

"Don haka idan har tsarin da ya dauƙi nauyin tsayar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya sabawa doka, to zaben tsayar da Bola Tinubu ma ya sabawa doka.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci