OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

An tsinci miliyan 8.7 da a wani hatsari a hanyar Kaduna

An tsinci miliyan 8.7 da a wani hatsari a hanyar Kaduna

Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kaduna, ta tabbatar da mutum daya ya mutu sannan uku sun samu raunuka a wani hatsarin mota da ya faru a hanyar Kaduna zuwa Abuja a daren Laraba.

 

A ranar Alhamis a Kaduna, Kwamandan hukumar Kabir Nadabo ya shaida wa NAN cewa an gano Naira miliyan 8.7 a wurin da hatsarin ya afku. 

 

A cewar Nadabo, hatsarin ya afku ne a kusa da Olam kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a daren Laraba da misalin karfe 23:01. 

 

Ya bayyana cewa wata mota kirar Golf Salon mai lamba SBG 87 XB da ta taho daga Minna a jihar Neja ta yi karo da wata tirela da ba ta da lamba a jiki a hanyar Kaduna. “Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa musabbabin hatsarin ya hada da gudun wuce sa'a, gajiya da kuma rashin kula, binciken da aka yi ya nuna cewa mutane shida hatsarin ya rutsa da su, mutum uku suka samu raunuka daban-daban, yayin da mutum daya, direban motar ya rasa ransa"

 

“An kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko Kaduna don ci gaba da kula da su,” inji shi. 

 

Nadabo ya bayyana cewa Naira miliyan 8.7 da aka samu yana hanyar hukumar tana jiran tantance mamallakin su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci