OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Shugaba Tinubu yakai ziyarar aiki Netherlands

Shugaba Tinubu yakai ziyarar aiki Netherlands

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa kasar Netherlands inda ake sa ran zai gana da manyan jami’an gwamnatin kasar da kuma ‘yan kasuwa.

 

Wata sanarwar da ofishin sa ya fitar yace “Shugaba Tinubu zai shiga tattaunawa mai zurfi da firan Ministan kasar, tare da yin ganawa daban-daban tare da Mai Martaba Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima. Sarauniyar ita ce mai ba da shawara ta musamman ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya UNSGSA."

 

 Yayin da yake kasar Netherlands, shugaba Tinubu zai halarci taron kasuwanci da zuba jari na Najeriya da Holland wanda zai hada shugabannin gwamnatocin kasashen waje, "in ji sanarwar.

 

 Idan ba a manta ba shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa kasar Netherland a ranar Talata.

 

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun Tinubu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce: “A bisa gayyatar da Firan Ministan kasar Netherlands, Mark Rutte ya yi masa. Shugaba Tinubu zai tattauna da shi, tare da ganawa da Mai Martaba Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima "

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci