OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

El-Rufai ya shawarci Tinubu ya kori duk jami'in gwamnatin da baya aiki

El-Rufai ya shawarci Tinubu ya kori duk jami'in gwamnatin da

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya sauke duk wanda ya nada wanda ya kasa cika aikin sa.

 

El-Rufai ya ba da wannan shawarar ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri a ranar Litinin, inda ya bukaci shugaban kasar da ya kuma duba yiwuwar gyara wasu manufofinsa da ba su samar da sakamakon da ake bukata ba.

 

 “Kun nada mutum mukami kuma ba ya aiki kamar yadda ake tsammani, cikin salama ku gaya mishi baka bukatarsa yaje ya nemi wani aikin na daban" a cewar El rufai.

 

Ya bukaci alumma su zama masu yin addua ga shugabannin da suka zaba. “Abin da ya kamata mu yi a matsayinmu na ’yan kasa shi ne mu yi wa shugabanninmu addu’a don Allah ya yi musu jagora su yi abin da ya dace.” 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci