OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 3 Makonni da suka shude

Majalisa ta tabbatar da babu shirin dawo da Abdul Ningi a halin yanzu

Majalisa ta tabbatar da babu shirin dawo da Abdul Ningi a ha

Kakakin majalisar dattijai, Yemi Adaramodu, ya bayyana a ranar Litinin cewa, babu wata yarjejeniyar sirri da akayi ta mayar da dan majalisar da aka dakatar Abdul Ningi.

 

Adaramidu ya ce shawarar da Sanatoci 108 ne suka yanke ce kadai zata bayyana makomar Ningi.

 

 Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi kan gaskiyar ikirarin cewa shugaban majalisar dattawa, GodsWill Akpabio, ya yanke shawarar sasantawa da dakataccen dan majalisar a cikin sirri.

 

"A zaman majalisa Sanatoci Baki daya suka tattauna akan lefin da Ningi ya aikata, an kuma bashi damar kare kanshi amman daga karshe gaba daya Sanatoci 108 idan ka cire Ningi sun yarda ya aikata wannan laifi hakan yasa aka bashi dan gajeran hukuncin dakatar dashi na tsawon watanni uku daga ayyukan majalisa."

 

 "Saboda haka Sanatoci 108 ne kawai suka dauki wannan matakin ne zasu iya kiran Sanata Ningi da ya dawo," in ji shi.

 

 Adaramodu ya bayyana damuwarsa game da wakilcin mazabar Ningi a lokacin da aka dakatar da shi. “Yayin da za a iya haramta wa dan majalisar gudanar da ayyukan majalisa, har yanzu zai iya cigaba da gudanar da ayyukan mazabarsa. An hana shi halartar zaman majalisa, tarurrukan kwamitoci da sa ido, amma zai iya ganawa da mutanen mazabar sa yana iya yin taro da su, ya yi magana da su,” inji shi. 

 

Idan ba a manta ba a ranar 13 ga watan Maris ne Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku bisa zarginsa da ikirarin Yan majalisar sun karkatar da N3.7tn daga cikin kasafin kudin 2024.

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci