OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnan Kano ya halarci taron gwamnonin Arewa da ake gudarwa a kasar Amurka

Gwamnan Kano ya halarci taron gwamnonin Arewa da ake gudarwa

Gov. Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya isa kasar Amurka domin halartar wani gagarumin taron tattaunawa da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya.

 

 Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na fadar gwamnatin Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa a ranar Laraba. 

 

A cewar sanarwar, taron na kwanaki uku yana samun halartar gwamnonin Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger, Sokoto, Kebbi, Jigawa, da kuma jihar Filato.

 

 Taron a cewar sanarwar an shirya shi ne domin magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya “Tattaunawar zai baiwa Gwamnonin wasu jihohin da ke fama da rikici damar zurfafa fahimtar yanayin barazanar tsaro, yanayin tattalin arzikinta, da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya a Arewacin Najeriya". 

 

Yayin taron za'a tattauna akan hanyoyin kawo karshen matsalar tsaro ta hanyar tattaunawa da masalaha tsakanin bangarorin biyu

 

 Dokta Joseph Sany, mataimakin shugaban Cibiyar Aminci ta Afirka ta Amurka ne zai jagoranci wannan taron kuma zai mayar da hankali kan daidaita manufofi da kuma kula da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

 

Sanarwar, ta bayyana za'a kammala taron a ranar 25 ga Afrilu, 2024.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci