OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 3 Makonni da suka shude

An gurfanar da malamin addinin da ya aikata fyade a gaban kotu

An gurfanar da malamin addinin da ya aikata fyade a gaban ko

Kotun Majistare ta Badagry dake jihar Legas ta gurfanar da wani malamin addini dan shekara 45 mai suna Sunday Adewoye a ranar Talata bisa zargin yi wa wata mata ‘yar shekara 22 fyade.

 

 Adewoye, wanda ba a bayyana adireshinsa ba, yana fuskantar tuhumar yin lalata da kuma aikata fyade.

 

 Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya, ya kauracewa jin ta bakin Adewoye, inda ya bayyana bukatar shawara da babban mai shigar da kara na jihar. 

 

Alkalin kotun ya bayar da umarnin a ajiye wanda ake tuhuma a gidan yari har zuwa lokacin da za a ba shi shawarar. 

 

Ya dage sauraron karar har zuwa ranar 3 ga watan Yuni. Tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Ayodele Adeosun, ya shaida wa kotun cewa Adewoye ya aikata laifin ne a ranar 17 ga Afrilu da karfe 5.00 na yamma a kan hanyar Joseph Dosu, Badagry.

 

Adeosun ya ce Adewoye ya yi lalata da matar mai shekaru 22 ba tare da izininta ba, wanda ya saba wa sashe na 260 da 263 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci