OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 3 Makonni da suka shude

Yansanda Imo sun kama wani matashi saboda mallakar bindiga

Yansanda Imo sun kama wani matashi saboda mallakar bindiga

Jami’an ‘yan sanda sun kama wani matashi dan shekara 31, Micheal Uzondu daga Amimo a karamar hukumar Ikeduru a jihar Imo bisa zarginsa da mallakar bindigogi.

 

 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, inda ya ce ya sayi bindigar ne daga hannun wani dan bindiga a Ugirike da ke karamar hukumar Ikeduru kuma yana da niyyar yin amfani da ita wajen kare kan shi.

 

 Rundunar ‘yan sandan ta ce, wani samame da jami’an sashin kula da miyagun kwayoyi na hukumar suka kai an gano wata maboyar ‘yan ta’adda da ke No 1 Titin Chidiobi Street, Site and Services, ya kai ga cafke matashin tare da kwato wata bindiga da kuma miyagun kwayoyi a hannunsa.

 

Ana ci gaba da gudanar da bincike, domin cafke dillalai da masu kera bindigogin.

 

" Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala gudanar da cikakken bincike,” inji Okoye. 

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aboki Danjuma ya yi kira ga mazauna jihar Imo da su baiwa ‘yan sanda sahihin bayanai domin dakile yaduwar muggan makamai da alburusai da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar baki daya.

 

CP Danjuma. Sanarwar ta kara da cewa, ta sake jaddada aniyar rundunar na inganta tsaro da jin dadin kowa da kowa a jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci