OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 3 Makonni da suka shude

Cosmos Ndukwe ya fice daga jamiyyar PDP

Cosmos Ndukwe ya fice daga jamiyyar PDP

Cosmos Ndukwe wanda tsohon dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar PDP ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar. 

 

A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP a mazabar Item C dake a karamar hukumar Bende a jihar Abia, Ndukwe ya bayyana dalilansa na kashin kansa da kuma yin tunani a kan burinsa na yanzu a matsayin sanadiyar ficewa daga jamiyyar.

 

An Kuma mika kwafin wasikar ga shugaban jam’iyyar da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa.

 

A cikin wasikar, Ndukwe ya bayyana cewa, “Bayan na yi nazari sosai, na cimma matsaya kan cewa ficewa daga PDP shi ne mafi dacewa a gare ni a wannan lokaci.” Ya kuma nuna godiya ga shugabancin jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi.

 

Ndukwe, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Abia ne, ya kuma mika godiyarsa ga kwamitin zartarwa na mazabar da daukacin ‘ya’yan jam’iyyar PDP na jihar Abia bisa goyon bayan da suka ba shi a duk lokacin da yake tare da jam’iyyar.

 

Ya kuma jaddada aniyarsa na bin tsarin dimokuradiyya hadi da cigaba da fafutukar samar da ci gaban jihar Abia.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci