OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnan Sokoto ya tube rawanin dagatai 15 a jihar

Gwamnan Sokoto ya tube rawanin dagatai 15 a jihar

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya amince da tsige dagatai 15 daga kan karagar mulki, bisa zarginsu da laifin rashin biyayya, satar filaye, taimakon rashin tsaro da kuma karkatar da kadarorin gwamnati.

 

 Sakataren yada labarai na gwamnan, Abubakar Bawa ne ya sanar da tsige dagatan da yammacin ranar Talata a wata sanarwa.

 

Dagatan da aka tsige sun hada da na Unguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, lllela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da gundumar Giyawa. 

 

Sauran sun hada da Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun Yar Tsakku, Sarkin Tambuwal da Sarkin Yamman Torankavwa,” inji sanarwar. 

 

Ya ce za'a Kara fadada bincike akan tuhumar da akewa dagatan Isa, Kuchi, Kilgori da Gagi.

 

Gwamnatin ta kuma yi wasu sauye-sauye Inda Sarkin Yakin Binji babban mai ba da shawara a Majalisar Sarkin Musulmi aka mayar da shi Bunkari yayin da Hakimin Sabon Birni aka tura shi Gatawa. 

 

Sanarwa ta kara da cewa gwamnatin zata cigaba da aiki da wasu dagatai bakwai da suka hada da Alhaji Aliyu Abubakar III Churoman Sokoto, Alhaji Ibrahim Dasuki Maccido Barayar Zaki, Abubakar Salame Sarkin Arewan Salame, and Aminu Bello Sarkin Yamman Balle.

 

Sai kuma Mahmoud Yabo Sarkin Gabas Dandin Mahe, Mukhtari Tukur Ambarura Sarkin Gabas Ambarura and Malam Isa Rarah Sarkin Gabas na gundumar Rarah, hadi da dagatan Tsaki da Asare.

 

Yayin da Abdulkadir Mujeli wanda aka nada a matsayin Magajin Garin Sokoto aka nemi ya koma kan mukaminsa na tsohon Sarkin Rafin Gumbi. 

 

Duk wannan sauye-sauye ya biyo bayan shawarwarin kwamitin lura da nade-naden sarakunan gargajiya, da sauya sunayen manyan makarantu da gwamnatin jihar ta kafa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci