OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

HURIWA tayi Allah wadai da kamfani mai na NNPCL

HURIWA tayi Allah wadai da kamfani mai na NNPCL

Kungiyar masu fafutukar kare hakkin dan adam ta Najeriya, HURIWA ta yi kakkausar suka ga kamfanin man fetur na kasa, NNPCL kan yadda yake tafiyar da matsalar karancin man fetur daya dabaibaye kasar a yan kwanakin nan.

 

A cewar wata sanarwa da kodinetan hukumar ta HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko ya fitar a ranar Talata, ta ce rashin iya aikin hukumar ta NNPC, ya baiwa yan bunburutu damar siyar da man fetur a farashi mai tsada a kusa da manyan gidajen mai da masu abun hawa ke buga dogayen layuka.

 

Onwubiko ya nuna matukar damuwarsa kan yadda hukumar ta NPL ta yi buris da alamuran da ke faruwa sanadiyar karancin man fetur din.

 

Yace abun takaici ne yanda yan bunburutu suka mamaye manyan tituna " harta a gaban hedkwatar kamfanin NNPC da kuma kusa da Transcorp Hilton da shugaba ya halarci wani taro kwanaki a Abuja akwai yan bunburutu "

 

 Yayin da masu ababen hawa ke fuskantar dogayen layi tare da tsawaita zaman jira a gidajen mai domin cika tankunansu. 

 

Sanarwar ta HURIWA ta yi Allah-wadai da hukumar NNPCPL bisa gazawarta wajen samar da man fetur yadda ya kamata ga al’umma, lamarin da ya haifar da karanci da ke baiwa ‘yan bunburutu damar cin gajiyar lamarin. 

 

Hakan ya haifar da cikas ga masu ababen hawa da kuma karin kudin sufuri a garuruwa irin su Abuja da Legas. 

 

Kungiyar ta kuma soki rashin sanya ido da Majalisar Dokoki ta kasa ke yi, tana mai cewa ya bai wa hukumar ta NNPC damar ci gaba da cin karanta babu babbaka.

 

Wannan a cewar HURIWA, ya kara ta’azzara matsalar man fetur da ake fama da shi a halin yanzu, duk da sauye-sauyen da NNPCL ta yi a baya-bayan nan zuwa kamfani mai zaman kansa, HURIWA ta lura cewa kamfanin na ci gaba da haifar da karancin man fetur da ake fama da shi.

 

 Kungiyar ta kuma yi tsokaci kan mummunan matsin rayuwar da ‘yan Najeriya ke fuskanta inda sama da gidaje miliyan 133 suke fama da matsanancin talauci.

 

HURIWA ta karkare bayanin nata da yin Allah wadai da gwamnatin tarayya na barin ‘yan bunburutu su karbe sayar da man fetur a kasar, a daidai lokacin da ‘yan Najeriya da dama ke fama da matsanancin talauci da kuma rashin tallafin gwamnati domin rage radadi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci