OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da layin dogon dake hanyar Fatakwal zuwa Aba

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da layin dogon dake hanyar Fat

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da layin dogo na zirga-zirgar jiragen kasa a kan hanyar  Fatakwal zuwa Aba.

 

 Ministan Sufuri, Said Alkali, ya kaddamar da jirgin kasan a hukumance a kan hanyar Port-Harcourt-Aba mai tsawon kilomita 62 a birnin fatakwal.

 

 Minista Alkali ya jaddada mahimmancin wannan cigaba inda yace ya dace da kokarin gwamnati na bunkasa kasuwanci, inganta zirga-zirga, da tabbatar da cudanya tsakanin alummar yankuna daban-daban.

 

Aikin farfado da hanyar jirgin kasan da aka baiwa kamfanin China construction ya hada da gyaran layin dogo da ake da shi, da gina tashoshi na zamani, da sayan sabbin kayan aiki.

 

Wannan shiri na da nufin saukaka jigilar kayayyaki a hanyar data hada da muhimman tashoshin jiragen ruwa da inganta harkokin tattalin arziki tsakanin yankuna. 

 

Yunkurin da Gwamnatin Tarayya ta yi na aiwatar da aikin ya hada da bayar da kashi 15% na kudin ginin, yayin da ta aro sauran kashi 85% na kudin daga bankuna.

 

Ana sa ran layin dogon daga Fatakwal zuwan Aba zai tallafawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

 

Minista Alkali ya jaddada aniyar gwamnati na kammala aikin cikin gaggawa domin bunkasar tattalin arziki. 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci