OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 10 A Kaduna

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 10 A Kadun

Dakarun ‘Operation Forest Sanity’ sun yi nasarar ragargazar ‘yan bindiga da ba a tantance adadin su ba a kananan hukumomin Chikun da Igabi na jihar Kaduna.

Sojojin sun kuma tarwatsa sansanonin ‘yan bindiga da ke karamar hukumar Chikun a yayin samamen da suka Kai. 

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan: “An kai farmakin har zuwa tsaunin Dakwala da Kunai da ke karamar hukumar, inda aka wargaza wasu maboyan, duk da cewa ba a gamu da ‘yan bindigan ba.

“Haka zalika an wargaza wani sansani a wani wuri da aka fi sani da ‘Daban Lawal Kwalba’ a karamar hukumar Igabi, bayan da sojojin suka ragargaji ‘yan bindigan da ke gadin wadanda aka yi garkuwa da su."

Dakarun da ke aikin sharan fage sun kutsa sansanin tare da ceto wasu mutane goma da aka yi garkuwa da su daure da igiya da kuma kaca. 

A cewar sanarwar: “Sojojin sun kwance mutanen da aka yi garkuwa da su, wadanda aka gano kamar haka.

- Surajo Aliyu

- Ayuba Yakubu

- Ibrahim Abdulrashid

- Aliyu Mohammed

- Magaji Tasiu

- Nasiru Ahmed

- Muhammad lbrahim

- Ayuba Abdulsalam

- Kelvin Musa

- Paul Patrick

"Rundunar sojojin da aka kara kai wa hari a cikin dungurmin dajin, sun yi nasarar kwashe mutanen da suka ceto zuwa wani wurin Sojoji inda ake kula da lafiyar su kafin a sake hada su da iyalen su."

Aruwan ya ci gaba da bayanin cewa sojojin sun kuma sake tarwatsa wani sansani a Rafin Gwaska a karamar hukumar Igabi tare da kwato makamai da kayayyaki.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da: Bindigogi guda uku na gida, Mujallar AK-47 guda daya, babban murfin AK-47 guda daya, cajan rediyon Bafoeng hudu, wayoyin hannu guda goma sha daya, akwatunan kida guda uku, rigunan soja guda biyu, Jaket guda daya, Sipanu, wukake da sarƙoƙi.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya yaba wa sojojin bisa ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

A halin da ake ciki a cewar sanarwar: "An shawarci 'yan garin da kada su ba da agajin jinya ga mutanen da ake zargi da ke dauke da abin da ka iya zama raunukan harbin bindiga.

“A nan take za a kai rahoton irin wadannan zargi zuwa dakin ayyukan tsaro ta layukan 09034000060 da 08170189999.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci