OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kwace Wayoyin Jami'an A Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kwace Wayo

Bandits

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ofishin ‘yan sanda tare da kwace wayoyin jami’an su a garin Magami da ke jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne a yau da misalin karfe 3:40 na rana kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.

Garin na daya daga cikin wuraren da aika-aikan ‘yan bindiga suka fi kamari, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin kaurace wa gidajen su.

A halin da ake ciki, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wani dan jarida mai suna Abdul Balarabe ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar sa: “’Yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda na yankin Magami dake karkashin karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wayoyi da wasu kayayyaki masu muhimmanci na ‘yan sandan da ke bakin aiki, sun kuma yi harbe-harbe sannan suka tsere.

"Lamarin ya faru ne a yau da misalin karfe 3:40 na rana."

Wasu majiyoyi a yankin ma sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka kara da cewa ‘yan bindigan sun kai hari ofishin ne domin su sako daya daga cikin su da aka tsare tun farko.

Sai dai kuma tuni aka mika wanda ake zargin zuwa hedikwatar ‘yan sandan jihar kafin lokacin da suka kai harin.

"Sun tattara wayoyin dukkan jami'an da ke bakin aiki da na daya daga cikin masu korafin da suka hadu a wurin, amma ba su kashe kowa ba," in ji wata majiya.

Yayin da babu wata sanarwa a hukumance kan lamarin daga rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Muhammad Shehu ya musanta rahoton ga Daily Trust.

Ya ce, "Babu irin wannan abu da ya faru" yayin da ya ki amsa wasu tambayoyi kan lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci