OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dalilin Da Yasa Nake Bikin Mauludi Duk Da Ni Kirista Ne - Fasto 

Dalilin Da Yasa Nake Bikin Mauludi Duk Da Ni Kirista Ne - Fa

Wani fasto mazaunin Kaduna Fasto Yohana Buru ya bayyana dalilin da ya sa yake gudanar da Mauludi tare da Musulmi a jihar.

A cewarsa, akwai musulmin da a koda yaushe suke tare da shi a cocinsa a watan Disamba domin murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu.

Faston  ya bayyana haka ne a wajen tattakin Mauludin da Babban Malamin addinin Islama na Kaduna, Sheikh Abdullahi Mai Barota ya shirya a unguwar Tudun Wada domin tunawa da Maulidin Manzon Allah.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito faston yana cewa duk shekara yana halartar bukukuwan Mauludi daban-daban sama da 25 zuwa 30 a fadin Najeriya.

“Mu Kiristoci ne kuma Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafe mu damu zama masu kula da ƴan uwanmu.  

"Na yanke shawarar shiga cikin ƴan uwana musulmi duk shekara domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabin Musulunci, Sallallahu Alaihi wa sallam.

"Wani dalili kuma shi ne saboda Musulmai ma suna tare da mu kowace shekara don yin bikin haihuwar Kristi a ranar Kirsimeti a cocina," in ji shi.

Fasto Buru ya ce yin Mauludi bana Musulmi bane kawai domin Annabi na kowa ne ba tare da la’akari da kabila, addini, al’adu da tarihi ba.

Ya ce manufar ita ce a ƙarfafa zaman lafiya da kuma juriya na addini a tsakanin mabiya addinan biyu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci