OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rikicin PDP: Na Amince Da Takarar Atiku, Okowa—Wike

Rikicin PDP: Na Amince Da Takarar Atiku, Okowa—Wike

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ya amince da jam'iyyar PDP, ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma mataimakinsa, Gwamna Ifeanyi Okowa, amma ba zai taɓa amincewa da shugaban jam'iyyar na ƙasa ba.

Wike yace bazai taɓa amince Sanata Iyorcha Ayu ya ci gaba da zama a ofis ba kafin zaɓen 2023, cewar Jaridar Vanguard.

Wike ya bayyana hakane a lokacin da ya karɓi bakoncin dan takarar gwamnan jihar Cross River na jam’iyyar PDP a ranar Laraba.

Da yake jawabi ga baƙinsa tare da Mataimakin Shugaban Kudu-maso-Kudu na Ƙasa, Cif Dan Orbih, wanda ya halarta, Wike ya  ce “Akwai masu taurin kai da kyamar adalci, gaskiya da daidaito a cikin jam’iyyar.

“Mun gama zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa, Muna da ɗan takarar shugaban ƙasa.  

"Wike ba cewa yayi a cire ɗan takarar shugaban ƙasa ba,  Wike cewa yayi a cire ɗan takarar mataimakin shugaban kasa?  To, me kuke roƙona?

“Abin da nake cewa, zan ci gaba da cewa kun ɗauki shugaban ƙasa, to ya kamata a bamu shugaban jam'iya, amma ba wanda yake so ya faɗi gaskiya.  

"Idan na ce a cire dan takarar shugaban kasa a cire mataimakin shugaban kasa, to za ka ce me ya sa nake yin haka.

“Na yarda da ɗan takarar shugaban ƙasa, na yarda da ɗan takaram mataimakin shugaban ƙasa, menene matsalar kuma."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci