OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Atiku Ya Tafi Ƙasar Amurka Don Cigaba Da Yaƙin Neman Zaɓe

2023: Atiku Ya Tafi Ƙasar Amurka Don Cigaba Da Yaƙin Neman

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya garzaya ƙasar Amurka domin ci gaba da yaƙin neman zaɓensa na 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa tafiyar yaƙin neman zaɓe ne na tsawon mako guda.

Yayin ake saran kuma Atikun zai gana da ƴan Najeriya da manyan ƴan kasuwa dake ƙasar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai tattauna da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje a wani bangare na shirye-shiryensa da ayyukansa a lokacin da yake ƙasar.

Sa'annan akwai zama da kuma tattaunawa ta musamman da ƴan jam’iyyar PDP a Arewacin Amurka.

Atiku zai gana da jiga-jigan ƴan kasuwan Najeriya da ke Amurka da kuma kwararrun matasa a ƙasashen waje.

Ana sa ran dawowarsa Najeriya a ranar Litinin kuma zai ci gaba da yaƙin neman zaɓensa a jihar Ekiti a ranar Talata 1 ga Nuwamba, 2022.

A ranar Laraba 2 ga watan Nuwamba ne kuma zai cigaba da gangamin yaƙin neman zaɓen PDP a jihar Ondo.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci