OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Masu garkuwa sun kashe wani malamin jami'a a jihar Ogun

Masu garkuwa sun kashe wani malamin jami'a a jihar Ogun

Wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun harbe wani malama a jami’ar Babcock Olowojobi Yinka har lahira a karamar hukumar Iperu ta jihar Ogun.

 

Musu garkuwa da mutanen sun harbi marigayin a kirji da ya fito shan iska a ranar Juma’a da misalin karfe 9:20 na dare a Ajadeh Event Centre bayan ya ki binsu kamar yadda suka bukata.

 

A cewar wani shaidan gani da ido da ya bayar da labarin faruwar lamarin, wasu mutane takwas sanye da bakaken kaya dauke da bindigu ne suka shiga dakin shakatawar, inda suka bude wuta tare da yin awon gaba da wani manajan gurin sayar da mota mai suna Dare da kuma wani mutum daya wanda har yanzu ba a samu sunansa ba.

 

Da take tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun ‘yan sandan Odutola Omolola, ta bayyana cewa an kai malamin asibitin koyarwa na jami’ar Babcock, inda aka tabbatar da mutuwarsa

 

Ta bayyana cewa an kama jami’in tsaron wajen shakatawar Awada Ishaya dan asalin jihar Filato, wanda aka dauke shi aiki makonni biyu da suka wuce lokacin da aka bude wajen shakatawar domin fadada bincike.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci