OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Wike Ya Marawa Gwamna Sanwo-Olu Na Legas Baya Maimakon  PDP

2023: Wike Ya Marawa Gwamna Sanwo-Olu Na Legas Baya Maimakon

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, a jiya, ya mara wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas baya a karo na biyu, amma ya yi shiru kan makomar ɗan takarar jam’iyyar adawa ta PDP.

Ɗan takaran PDP a jihar Legas wato Dr Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor, bai samu goyon bayan Gwamna Wike ba.

Gwamna Wike ya yi jawabi ne a matsayin babban baƙo na musamman a taron shekara-shekara na mata a jihar Legas na shekarar 2022, mai taken ‘Spring Forth, Stand Out,’ da aka gudanar a Eko Hotel and Suites, Legas.

Gwamnan ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 300 ga kwamitin matan masu muƙamai a matsayin tallafi.

Yayin da yake mara bayan ga Sanwo-Olu a karo na biyu, gwamnan Rivers ya ce: “Da yardar Allah za ka zama gwamna a karo na biyu.  

"Jihar Legas ta fi sauran jihohin ƙasar nan, saboda Legas ta bai wa mata damar shiga harkokin mulki ta fannoni daban-daban.  

"Ina farin cikin shiga wannan taro, ruwaitowar Jaridar Vanguard.

“Ba na wasa da siyasar ƙabilanci, Ko da Sanwo-Olu yana jam’iyyata amma baya yin abu mai kyau, da ban zo ba.  

"Ba na nadamar cewa ina goyon bayanka.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci