OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Ministan makamashi a Saliyo yayi murabus sanadiyar matsalar wutar lantarki

Ministan makamashi a Saliyo yayi murabus sanadiyar matsalar

Alhadji Kanja Sesay

Ministan Makamashi a Saliyo ya yi murabus a ranar Juma'a sakamakon katsewar wutar lantarkin da aka samu a kasar. 

 

Ko da yake ba a bayyana dalilin da ya sa Alhadji Kanja Sesay ya yi murabus a hukumance ba, kuma ma'aikatar makamashi ba ta amsa bukatar yin sharhi daga AFP ba. 

 

An mika ragamar gudanar da ma'aikatar karkashin kulawar Shugaban kasa Julius Maada Bio kai tsaye, wanda wasu jami'ai biyu za su taimaka masa, kamar yadda wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta aikewa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a yammacin Juma'a ta sheda.

 

 Murabus din Sesay ya zo ne sa'o'i bayan gwamnati ta biya jimillar kudaden Dalar Amurka miliyan 18.5 ga kamfanonin samar da wutar lantarki guda biyu, Turkish Karpowership da kungiyar Transco-CLSG da suke bin kasar Sierra Leone bashin dala miliyan 40. Ba a dai fayyace ko murabus din Sesay na da alaka da biyan kudin ba.

 

Bayan watanni biyu da katsewa, an dawo da wutar lantarki a Freetown bayan an sanar da biyan kudaden, a cewar wani dan jarida na AFP.

 

Tun shekarar 2018 ne kamfanin Karpowership ne ke samar da wutar lantarkin ga kasar Saliyo daga wata na'ura mai yawo a teku, amma ya rage karfinsa daga megawatt 65 zuwa biyar kacal a 'yan watannin nan saboda gaza biyan kudi.

 

 "Mun yi farin ciki da tabbatar da cewa cikakkiyar wutar lantarki ta dawo a Freetown," in ji kamfanin yan Turkiyya a cikin wata sanarwa data biyo da sanar da sabon biyan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci